Jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki na biyu na kasar Sin ya shiga teku
An gudanar da bikin murnar shigar da jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki na biyu mallakar kasar Sin ruwan teku da safiyar yau Laraba, a birnin Dalian dake kasar Sin, inda memban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma mataimakin shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na JKS janar Fan Changlong ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.
Kasar Sin ta kera wannan jirgin ruwan yaki ne na kanta, an kuma fara kirar sa a watan Nuwanba na shekarar 2013. Yanzu haka an kammalar aikin kera shi da ajiye na'urorin tsarin samar da makamashin wutar lantarki, sannan za a ajiye tsarin makamai bisa shirin da aka tsara, kana za a yi gwajin ayyukansa, yayin da jirgi ke sashen mashigin teku. (Zainab)