in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta horas da hafsoshin da za a jibge a kasashen Sudan da Sudan ta kudu
2016-11-01 18:41:17 cri
Ofishin kula da harkokin tabbatar da zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bude wani kwas din horas da hafsoshi da muhimman sojoji 90 na rundunar tabbatar da zaman lafiya wadanda za a jibge su a kasashen Sudan ta kudu da yankin Darfur na Sudan nan ba da dadewa ba.

Abubuwa biyar ne aka koyarwa hafsoshin daga ranar 26 ga watan Oktoba zuwa yau 1 ga watan Nuwamba, kamar ka'idojin wasu takardun MDD, ciki har da "takardar fahimtar juna ta MDD" da "littafin ba da jagoranci ga kasashe wadanda suke tura sojojinsu aikin tabbatar da zaman lafiya" da yadda ake kare 'yan gudun hijira da dai sauransu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China