A ranar litinin 1 ga wata, ma'aikatar tsaron kasar Sin ya shirya taron manema labaru, inda Mr. Yang Yujun ya ce, a wannan karo, an canja tsoffin hukumomin sojoji 7, kuma an kafa hukumomin yankunan yaki guda 5, kuma kwamitin tsakiya na soji na kasar Sin ya shugabanci wannan aiki. An kafa hukumomin yankunan yaki don ba da umurni wajen yake-yake cikin hadin gwiwa tsakanin rundunoni na yankuna daban daban, da gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da tinkarar kalubalen da ake fuskanta, ta yadda za a cimma nasara duk lokacin da wani yaki ya barke.
Yang Yujun ya ce, yanzu, an kammala aikin kafa hukumomin yaki a yankunan daban daban na kasar.
Ya kara da cewa, a kullum kasar Sin tana bin manufar tsaron kai, kuma za ta tashi tsaye don gudanar da wannan manufa, ko ta kaka ba zata canja wannan manufa ba.(Bako)