A jawabinsa mamban majalisar gudanarwar kasar kuma ministan tsaron kasar Chang Wanquan ya bayyana cewa, raya sojojin dake dacewa da matsayin kasar da moriyar kasar a fannonin kiyaye tsaro da samun bunkasuwa shi ne muhimmin abin da ke gaban kasar Sin yayin da ake kokarin raya kasa mai tsarin gurguzu na zamani.
Chang Wanquan ya yi nuni da cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da tabbatar da zaman lafiya da bada gudummawa ga samun bunkasuwa a duniya da kuma tabbatar da dokokin kasa da kasa.
Sin tana son kara hada kai da sauran kasashen duniya, da sa kaimi ga raya sabuwar dangantakar hadin gwiwa ta samun moriyar juna a tsakaninta da kasashen duniya, da yin kokarin cimma buri iri daya na dan Adam. Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin kiyaye tsaro na kare kanta da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasar da na sauran kasashen duniya, da shiga harkokin kiyaye tsaro na kasa da kasa da yankuna, kuma tana son samar da kayayyakin kiyaye tsaro a fannonin aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, yaki da ta'addanci, bada kariya ga jiragen ruwa, bada ceto bayan barkewar bala'i da dai sauransu. Kana Sin tana tsayawa tsayin daka kan tabbatar da kare 'yancinta da tsaro da moriyar bunkasuwarta, da tabbatar da cikakken yankin kasar da moriyar tekunta, ta kuma yi imani da samun karfi wajen tinkarar duk wata barazanar tsaro. (Zainab)