Shirin wanda ake fatan zai fara aiki cikin watan Satumban wannan shekara zai hade ragowar matakan bayar da dauki ta hanyar amfani da muhimman bayanai, bincike da shirin mayar da irin wadannan mutane yankunansu na asali da tsugunawar da kuma hade dukkan rukunin mutanen da batun ya shafa.
Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo shi ne ya bayyana hakan a Abujar,fadar mulkin kasar yayin da yake jawabi albarkacin ranar tunawa da 'yan gudun hijira ta duniya ta shekarar 2017,
Osinbajo, ya ce sabon shirin zai mai da hankali wajen daukar matakai na zahiri masu dorewa maimakon matakan dogaro a kan kayan agaji. A cewarsa, shirin ya nuna kudurin gwamnatin kasar na daukar kwararan matakai da za su kai ga magance matsalolin da mutanen da rikici ya raba da muhallansu.
Ya ce,Najeriya ta himmatu wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati da cimma da kasar Kamaru da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) game da dawo da 'yan gudun hijirar kasar ta Najeriya dake zaune a Kamaru bisa radin kansu.(Ibrahim)