in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tsaurara matakan tsaro a lokacin bukukuwan karamar sallar bana
2017-06-25 13:08:05 cri

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara tsaro ta hanyar tura jami'an 'yan sanda masu yawan gaske a duk fadin kasar a lokacin gudanar da bukukuwan karamar salla ta wannan shekara.

Babban sifeton 'yan sandan kasar, Ibrahim Idris, ya bayyana cewa tun a ranar Juma'a ne hukumar ta tura jami'an 'yan sandan yankuna daban daban tun gabananin fara bukukuwan karamar sallar a yau Lahadi.

Mai Magana da yawun 'yan sandan Najeriyar Jimoh Moshood, ya fada cewa jami'an nasu zasu gudanar da aikin tabbatar da tsaron ne a wuraren shakatawa, da wuraren taruwar jama'a, da muhimman kayayyakin more rayuwa da sauran gine ginen gwamnati.

Ya ce an kuma baza jami'an a manyan titunan kasar don su sa ido, an kuma tanadi jami'ai masu yaki da bata gari wadanda aka tura su manyan hanyoyin mota na kasar.

Moshood ya ce, jami'an 'yan sanda za su tabbatar da tsaurara tsaro, kana za su gudanar da ayyukansu ta hanyar kyakkyawan mu'amala da fahimtar juna tsakaninsu da sauran jama'a a lokacin da suke bakin aiki.

Ya ce an tura jami'an wuraren da ake fargabar faruwar wani rikici ko tashin hankali.

A jihar Borno shiyyar arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici, hukumar 'yan sandan ta sanar da takaita zirga zirgar ababawan hawa a lokutan gudanar da shagulgulan bikin karamar sallar, musamman a birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere dake jihar.

Victor Isuku, mai Magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ya ce, wannan haramcin zirga zirgar ababen hawar ya shafi motoci, da babura masu kafa uku, da kuma babura har ma da dawakai, sai dai hanin bai shafi jami'ai masu aiki na musamman ba.

Ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon barazanar tsaro ta baya bayan nan, kana an bukaci al'ummar musulmi da su gudanar da sallar idin ne a filayen idi mafi kusa da gidajensu.

Kana ya shawarci al'umma da su sa ido don tabbatar da tsaro, kuma su kai rahoton duk wata bakuwar fuska da ba su amince da ita ba ga jami'an tsaro.

Wannan shi ne karon farko da aka haramta zirga zirgar a jihar Borno, tun a shekarar 2015, a lokacin da jami'an sojin kasar suka yi galaba kan mayakan Boko Haram.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China