in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya kafa majalisar zartaswar kasar
2017-05-31 11:01:41 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kafa majalisar zartaswa mai mambobi 19 a ranar Talata, kwanaki 143 bayan ya kama aiki.

An sanar da sunayen kananan ministocin kasar ne a zauren majalisar dokokin kasar, inda shugaban majalisar dokokin kasar farfesa Michael Aaron Oquaye ya sanar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bukaci hakan.

Shugaban ya sha fuskantar matsin lamba daga bangaren marasa rinjaye a majalisar game da sunayen ministocin da ya gabatar a majalisar watanni uku da suka gabata.

Kundin tsarin mulkin kasar ta Ghana ya amince shugaban kasar ya gabatar da sunayen ministocin kada adadinsu ya kasa 10, kuma kada yawansu ya wuce 19. Ita dai majalisar zartaswar zata tallafawa shugaban kasar ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan da suka shafi sha'anin gudanar da mulki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China