Da yake jawabi yayin bude taron nahiyar Turai kan samun ci gaba na 2017 a Belgium, babban taro dake inganta hadin kan kasashe da samar da ci gaba, Akufo Addo ya ce yawan adadin matasa a cikin al'umma na da dimbin dammakin samar da ci gaba cikin kankanin lokaci.
A cewarsa, tsarin tattalin arzikin Ghana kamar na sauran kasashen nahiyar Afrika, na nan yadda yake tun bayan zamanin mulkin mallaka, inda ya dogara kan fitar da kayayyaki, yana mai bada misali da Ghana dake fitar da zinare da Cocoa da katako.
A cewar sanarwar da fadar Flagstaff ta shugaban kasar Ghanan ta fitar, shugaban ya ce ba za a samu ci gaba cikin gajere ko matsakaici ko dogon zango a yammacin Afrika ba, muddun aka ci gaba da tafiyar da tattalin arziki na yadda yake.
Akufo Addo ya ce abun da gwamnatinsa ta fi mai da hankali a kai shi ne, samar da tsarin tattalin arziki da zai karbu ga kowa a Afrika, wanda kuma zai samar da aikin yi da kwanciyar hankali ga al'umma. (Fa'iza Mustapha)