in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kwadago a Sudan ta kudu ta nemi karin albashi duk da matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki
2017-05-02 10:08:55 cri
Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasar Sudan ta kudu ta bukaci gwamnatin kasar da ta aiwatar da alkawarin da ta dauka na karawa ma'aikatan gwamnati a kasar albashi da ninki uku, sannan a inganta yanayin aiki a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu a kasar.

George Paul Baya, shi ne jami'in hulda da jama'a na kungiyar kwadago ta kasar, ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta gaza aiwatar da cikakken alkawarin da ta dauka, kasancewar ma'aikatan gwamnatin tarayya ne kadai suka samu cikakken albashi yayin da ma'aikatan kananan hukumomi da hukumomin da ba na gwamnati ba, babu abin da ya sauya duk kuwa da tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

Baya ya zargin gwamnati da gazawa wajen daidaita al'amurra a bangaren hukumomin da ba na gwamnati ba, inda ya bayyana cewa suna matukar bautar da ma'aikatansu fiye da kima.

A cewarsa sun bukaci gwamnati da ta yi iyakar kokarinta wajen inganta rayuwar ma'aikata a duk fadin kasar. Sannan ya ce dole ne dukkan shugabanni su yi wa wadanda ke aiki a karkashinsu adalci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China