Shugaban hukumar zartaswar kungiyar Moussa Faki Mahamat, shi ne ya yi wannan kira, cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Lahadi. Mr. Mahamat ya ce kamata yayi tsagin gwamnatin hadin kan kasar da na 'yan adawa, su daina kaiwa juna farmaki, musamman ma a yankin jihar Upper Nile inda al'amura suka fi ta'azzara.
Ya ce tashe tashen hankula dake faruwa a kasar, na ci gaba da haifar da koma baya a fannin tsaron kasa, tare da barazana ga rayukan al'ummar kasar baki daya.
Daga nan sai ya bukaci dukkanin sassan da ba sa ga maciji da juna, da su martaba dokokin kasar, da ma yarjejeniyar da aka cimma game da warware rikicin siyasar Sudan ta kudun.(Saminu Alhassan)