A jiya Laraba ne aka kaddamar da jerin shirye-shirye da bankin kula da kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar da kuma kasashen waje wato Afreximbank ya shirya a wani bangare na taronsa shekara-shekara, a birnin Kigali.
Ana sa ran shirye-shiryen na yini 4 da za su samu halartar masu gabatar da mukala sama da 100 da malamai da masana harkokin kasuwanci na duniya, za su zama wata hanya ta bunkasa tsare-tsaren cinikayya a nahiyar Afrika
Babban masanin tattalin arziki kuma dirktan sashen bincike da kula da hadin kan kasashe na Bankin Hippolyte Fofack, ya ce bankin Afriexim ya kaddamar da wani muhimmin shiri da zai magance tsoffi da sabbin kalubale da kasashen Afrika ke fuskanta a lokacin da suke fafutukar neman ci gaba.
A cewarsa, ana sa ran a bana, alkaluman tattalin arziki na GDP a nahiyar zai karu da kimanin kashi 3. Inda ya ce ana samun ci gaba a nahiyar ne ta hannun wasu kasashe dake zuba jari kan harkokin da suka shafi ababen more rayuwar al'umma, da nufin domin kara baza komar tattalin arziki da kuma samun mafita daga faduwar farashin mai. (Fa'iza Mustapha)