Ministan cinikayya, masana'antu da zuba jari na kasar Okechukwu Enelamah ne ya bayyanawa manema labarai hakan, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar da ya gudana karkashin mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo.
Ministan ya ce ofishin zai rika kula da harkokin da suka shafi cinikayya a ma'aikatu, hukumomi da sauran sassan gwamnati, da a baya, ba ya samun kulawar da ta dace.
Ya kara da cewa, ofishin zai kasance karkashin shugaba da matakin aikinsa ya kai na Jakada, wanda zai rika aiki tare da majalisar da kuma ayarin kwararru masu kula da harkokin tattalin arzikin kasar.
Har ila yau, Okechukwu Enelamah ya ce zai zama wata muhimmiyar hanya ta shiga tattaunawa kan yarjejeniyoyin samar da yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar da ma yarjeniyoyin cinikayya da abokan hulda a sauran kasashen duniya.
Ministan ya ce gwamnatin na son ta magance matslolin cinikayya da ake samu da suka hada da jibge kayayyaki marasa inganci da sauran wasu batutuwa ta yadda su dace da na sauran kasashen duniya. (Fa'iza Mustapha)