Dr. Kiptoo wanda ya shaidawa mahalarta wani taron shiyya hakan yau Talata a birnin Nairobin kasar Kenya, ya kara da cewa kere keren fasaha, na bada damar gaggauta hidimomin da suka jibanci shige da ficen hajjoji ta kan iyakokin kasashe, wanda hakan ke rage kudaden da ake kashewa, yayin hada hadar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.
Kiptoo dai na wannan tsokaci ne yayin taro na 14, na kwamitin manyan jami'ai, da babban taron mambobin gamayyar masu ruwa da tsaki, kan batutuwan da suka shafi cinikayya ta yanar gizo da aka yiwa lakabi da AAEC.