Olusegun Awolowo, shine babban daraktan majalisar inganta harkokin fitar da hajoji zuwa ketare NEPC, ya shedawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, wannan mataki ya biyo bayan irin nasarorin da aka cimma ne a sha'anin saukaka hanyoyin kasuwanci da kuma rage lokacin da ake batawa wajen fitar da kayayyaki daga Najeriya zuwa kasashen waje.
Awolowo yace wannan na daga cikin yunkurin da hukumar NEPC take yi wajen samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ta hanyar saukaka hada hadar cinikayya ta cikin gida da kuma na kasa da kasa.
Yace Najeriya ta kasance kasa ta 107 a matsayin mamba a kungiyar kasuwanci ta kasashen duniya (WTO), inda ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zama mambar a karkashin yarjejeniyar cinikayya ta (TFA) a birnin Davos.
Yace rahoton baya bayan nan da bankin duniya ya fitar ya nuna cewa Najeriyar ta samu cigaba kadan, inda ta tashi zuwa kasa ta 149 maimakon kasa ta 160 a baya cikin jerin kasashen duniya 190.
Mr. Awolowo, yace UN/CEFACT zata taka muhimmiyar rawa wajen amfanar da kananan 'yan kasuwa wajen saukaka fannin hada hadar kasuwanci da sauran batutuwa da suka shafi ciniki.