Darakta Janar na Hukumar UPU Bishar Hussein ya shaidawa wani taro kan harkokin sadarwa ta wayar tarho a Nairobi cewa, kafar da aka yi wa lakabi da Ecom@Africa, za ta samar da dimbin dammamakin kasuwanci ga 'Yan Afrika a duniya.
Ya ce sun lura cewa, an bar nahiyar Afrika a baya a fannin cinikayya ta intanet da ake yi a duniya, a don haka, kafar za ta ba nahiyar damar bin sahun sauran kasashen duniyar ta fuskar bunkasa harkokin cinikayya.
Hukumar ta zabi wasu kasashen da dama da take son fara shirin da su, da niyyar daga bisani, za ta hade su baki daya ta yadda za a samu cibiyar kasuwanci ta intanet a fadin nahiyar.
Kasashen da ta zaba sun hada da Kenya, da Afrika ta kudu, da Kamaru, da Cote d'ivoire, da Morocco, da kuma Tunisia. (Fa'iza Mustapha)