Shugabannin gwamnatoci da kamfanonin kasashen Afrika sun yi kira da a kara zuba jari a Afrika domin karfafa bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar.
Shugabannin sun kaddamar da wannan kira a ranar Litinin a yayin bude wani dandalin zuba jarin Afrika a Kigali, babban birnin Rwanda.
Kasar Rwanda na karbar bakuncin wannan dandalin zuba jari na matsayin koli daga ranakun 5 zuwa 6 ga watan Satumba, bisa burin tallafawa kasuwancin kasa da kasa da zuba jari a Afrika.
Afrika ta kosa sosai wajen karbar zuba jari a bangarorin tattalin arzikinta da dama. Akwai makomar tattalin arziki da dama dake jiran a zuba jari daga mutanen cikin gida da na waje. Karuwar zuba jari za ta taimaka wajen gaggauta bunkasuwa a nahiyar, in ji shugaban kasar Uganda, Yoweri Kaguta Museveni.
Ana shirya wannan dandali a karkashin jagorancin kasuwar hadin gwiwar yankunan arewa da kudancin Afrika da gwamnatin Rwanda, wanda kuma ya janyo mahalarta kusan dubu guda, da suka hada da shugabannin kasashe da gwamnatoci, ministoci da shugabannin bangaren masu zaman kansu. (Maman Ada)