Wani kamfanin bincike na kasa da kasa mai suna Ernst & Young (EY) ya ce, akwai yiwuwar jarin da kasashen waje za su zuba kai tsaye wato (FDI) zai ragu nan da watanni 18 masu zuwa a yankunan kudu da hamadar Sahara, sakamakon wasu sauye sauyen dabarun kasuwanci da masu zuba jari za su gudanar.
A yayin gabatar da wani shirinsa na mataki na 3 na shekarar 2016 a birnin Johannesburg, EY ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne masu zuba jarin za su fi mayar da hankali kan yankunan da aka fi hasashen samun bunkasuwar tattalin arziki.
EY ya ce, manyan kasashe 3 mafiya karfin tattalin arziki a yankin kudu da hamadar Sahara wato Angola da Najeriya da kuma Afrika ta Kudu sun samu koma baya sakamakon kalubalolin da suke fuskanta. Kasashen dake yankunan gabashi, da masu amfani da harshen Faransanci, da na arewacin Afrika ne ake sa ran za su samu karuwar kashi 4 ko sama da haka.
EY ya ce, masu zuba jari daga yankin Asiya da Pasific sun fi shahara, kuma kasashen Sin da Japan ne ke kan gaba. Shiyyar ta biyu mafi girma, idan aka kwatanta da karfin jarin kasashen waje, da manyan ayyuka da kuma samar da ayyukan yi.
Kamfanin binciken ya kuma bayyana cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a Afrika ya karu zuwa kashi 209 a watanni ukun farko na shekarar 2016 idan aka kwatanta da na makamancinsa a shekarar 2015. Sannan manyan ayyukan more rayuwa da guraban ayyukan yi da aka samar a watanni ukun farko na shekarar 2016 ya fi wadanda aka samar tun a shekarar 2005. Sin ita ce kasa ta uku a duniya mafi zuba jari a nahiyar.(Ahmad Fagam)