Da suke gabatar da jawabai, a lokacin taron dandalin hadin gwiwa na bankin hada hadar kasuwanci na Afrika da gwamnatoci karo na 3, wanda aka gudanar a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, masanan sun jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da 'yan kasuwa domin hakan zai bada damar samun karuwar masu zuba jari daga kasashen waje.
Kasar Rwanda ce ta karbi bakuncin taron tsakanin ranakun 26 zuwa 27 ga wannan wata, mai taken; "dawwamamman tsari a Afrika: cigaba ta hanyar fasaha da hadin gwiwa"
Taron na kwanaki biyu, ya tabo muhimman hanyoyin da kasashen Afrika zasu ci gajiyar fasahohi, da batun hadin gwiwa a tsakanin kasashe, da hukumomin harkokin kudade, da kungiyoyi, ta yadda za'a gina kyakkayawan tsarin cinikayya ta hanyar hadin gwiwa tsakanin 'yan kasuwa da gwamnatoci.
Mahalarta taron sun hakikance cewa, muddin ana bukatar ingantaccen tsarin kasuwanci, ya zama tilas a tabbatar da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 'yan kasuwa da fannin tattalin arziki. Haka zalika, wannan hadin gwiwa ta shafi mu'amalar kasuwanci ta cikin gida da kuma kasashen ketere.