in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ITTF ta fidda sanarwar ficewar wasu yan wasa a yayin bude gasar kasar Sin
2017-06-28 16:08:06 cri
Hukumar shirya gasar wasannin kwallon tebur ta kasa da kasa (ITTF) ta fidda wata sanarwa game da wasu yan wasan kasar Sin 3 inda ta soke wasanninsu na Seamaster 2017 ITTF World Platinum China wanda aka bude a ranar Lahadi, tana mai cewa dukkan wani batu game da yiwuwar korarsu yana nan an tanadeshi.

Hukumar shirya gasar kwallon teburin ta kasa da kasa ta fada cikin wata sanarwa cewa, tana daukar wannan batu da muhimmanci kwarai da gaske.

Sanarwar tace, a halin yanzu, dukkan wasu batutuwa da suka shafi wannan hukunci yana nan an tattarashi, kuma ITTF zata cigaba da gudanar da bincike kafin ta yanke hukunci na karshe kan wannan al'amari.

Manyan yan wasan na duniya sune Ma Long, Fan Zhendong da Xu Xin, basu bayyana ba a wasanninsu zagaye na 16 a lokacin bude wasan a kasar Sin a ranar Juma'a.

ITTF ta fada cewa ta samu wasu bayanai takaitattu daga (CTTA) tare da neman afuwa daga tawagar yan wasan kwallon teburin ta kasar Sin, kuma tana jiran samun cikakken rahoto daga CTTA da kuma jami'an ITTF wanda yake tabbatar ainihin dalilan da suka sa yan wasan 3 basu halarci wasansu zagaye na 16 ba.

Gabanin gasar ta ranar Juma'a, yan wasan 3 da kuma kociyoyinsu Qin Zhijian da Ma Lin, sun wallafa bayanai a shafukansu na sada zumunta dake nuna cewa, "basa jin kamar suna yin wasa" saboda sun yi rashin tsohon kociyansu Liu Guoliang.

A ranar Talata, aka bayyana kociyan Grand Slam champion, Liu, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar wasan tebur ta kasar Sin (CTTA) kuma a yanzu ya kasance ba shine babban kociyan tawagar yan wasan tebur ta kasar Sin ba.

A bisa ga wannan sabon tsarin da aka fitar a ranar Talata, CTTA ta soke matsayin babban kociya da shugaban kociya a tawagar yan wasan kasar Sin, kuma a maimakon hakan, ta kafa wasu tawagogin kociyoyin yan wasa biyu na bangaren yan wasa maza da kuma na bangaren yan wasa mata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China