in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MLB tana neman bunkasa fannin wasan baseball na kasar Sin
2017-05-24 19:53:02 cri
A makon daya wuce dan wasan baseball na kasar Sin Gong Haicheng ya bayyana aniyarsa na kulla yarjejeniya da babbar kungiyar wasan League Baseball, amma kungiyar MLB ta yi amanna cewa akwai matasa masu yawa da zasu iya zama a sahun gaba a wasan baseball na duniya daga wannan kasa wadda tafi yawan jama'a a duniya.

Gong mai shekaru 18 a duniya shine matashi na biyu da ya rattaba hannu don yin aiki da kulob din League MLB dake kasar Sin. Akwai kuma takwaransa Xu Guiyuan, daga cibiyar wanda ya sanya hannu don yin aiki tare da Baltimore Orioles shekaru biyu da suka gabata.

A yanzu haka dai kasar Sin tana da yan wasa wadanda zasu iya yin wasa a matsayi na MLB, wannan wani babban mataki ne dake kan hanya mafi dacewa. Naga wasu makarantu masu zaman kansu masu yawa da kamfanoni dake daukar wasan baseball, wanda yake kara samu shahara a kasar Sin" janar manajan MLB Asia Rick Dell ne ya bayyana hakan

A matsayinta na daya daga cikin kasashe dake da karfin fada aji ta fuskar wasanni, kasar Sin ta zama tamkar madubi ga wasu kungiyoyin wasanni na kasa da kasa dake neman bunkasuwa a duniya. Domin burin da take dashi wajen kai wasan baseball zuwa babban matsayi a duniya don neman wasu kwararrun yan wasan, MLB ta fara shirye shiryenta a kasar Sin tun shekaru 10 da suka wuce.

Ga MLB, girman Gong da Xu, cigaba ne, kuma nasararsu tana nuna samun nasarar cibiyar bunksa wasannin ta kasar Sin.

A manufar da take dashi na kara samun shahara game da wannan wasa da samar da tauraron yan wasan daga kasar Sin, cibiyar samar da horo ta MLB ta kasar Sin ta bude makarantar Dongbeitang a Wuxia a shekarar 2009, da yan wasa na cikin gida 16. A yanzu haka MLB tana da cibiyoyin horaswa har guda 3 a kasar Sin, da sauran biyun a Changzhou da Nanjing.

Wadan nan cibiyoyin dukkansu suna da masu horas da yan wasan baseball na kasa da kasa. Daliban dake wannan makaranta suna samun horo da kuma darrusa a harshen turanci baya ga ilmin da suke samu mai inganci.

Game da labarin Gong, ba wai kawai batun kulla yarjejeniya da pirate bane, harma ya samu amincewa daga jami'ar kasa da kasa ta Shanghai. Don haka, zai cigaba da yin aiki har zuwa matakin digiri," inji Dell, wanda shine babban kociyan baseball a kwalejin New Jersey har tsawon shekaru 27 kafin daga bisani ya dawo kasar Sin domin sa ido game da shirin cigaba na MLB.

"Abinda ya nuna a yanzu shine, a yau za'a iya samun dalibi mai hazaka wanda zai iya yin fice a darasinsa na aji da kuma wasan ."

Gong, wanda yake karatu da kuma samun horo a cibiyoyin Changzhou da Nanjing, yace, yana sha'awar buga wasa a babbar kungiyar wasa ta Major League, wata rana.

"Ina son yin wasa a Major League, amma ya kamata na bi mataki zuwa mataki. Na taba zuwa Amurka. Yanayin wajen wasan baseball yana da ban sha'awa kuma matakin yayi nisa matuka. Ina bukatar yin aiki tukuru kuma ina korarin yin wasa a Major League," Gong ya tabbatar da hakan wanda zai yiwa kasar Sin wasa a gasar Baseball Classic ta duniya a shekarar 2017.

Ray Chang, kociyan Gong, a cibiyar Nanjing, yana da kyakkyawar fata game da aikin Gong a Amurka.

"Dukkanmu muna da tarihin wasan baseball na kasar Sin a halin yanzu. Gong yarone mai kyau, kuma ya samu hakan ne saboda yin aiki tukuru. Zai kasance ya samu wata kwarewace ta daban yayin wasa a Amurka saboda suna da kungiyar wasan baseball league mafi girma a duniya."

"Babbar shawarata ga Gong itace ya yi kankan da kai, kuma ya cigaba da yin aiki tukuru. Akwai abubuwa masu yawa da zasu iya katse hanzari ga kwarren masanin wasan na baseball, masu kyau da marasa kyau. Lallai ya kamata ka cigaba da abinda kake yi" inji Chang.

Baya ga aikin gudanar da cibiyoyin, MLB ta kaddamar da wani shirin horas da matasa wasan na baseball! A wasu manyan biranen kasar Sin, suna taimakawa dalibai sinawa na makarantun matakin farko wajen shigar dasu gasar wasannin baseball, da shigar dashi cikin manhajar karantar da daliban, da samar da lasisi 80 ga shagunan MLB a duk fadin kasar Sin, kuma ta samar da wasu tashoshin watsa shirye shiryen wasannin MLB a kasar Sin, da suka hada da MLB All-Star Game da na duniya.

Dukkan manufofin yin hakan shine domin bunksa harkokin wasanni da kuma samar da tsarin wasan baseball na Yao Ming, wanda ya fadada wasan kwallon Kwando a kasar Sin a lokacin da shahararren dan wasan na kasar Sin yayi wasa ga Houston Rockets a NBA.

Da aka tambaya shin ko kasar Sin zata iya samun Yao Ming na baseball, Dell yace.

"Na tabbata hakan zai iya faruwa. Hakan zai faru."

"Ina kasar Sin sama da shekaru 10. Ina ganin abubuwan da ban taba ganinsu ba. Na bar fannina a Amurka domin na zo nan na yi amanna da wasan baseball na kasar Sin.

"Yana daukar dogon lokaci wasan baseball, shi ba kamar wasan kwallon Kwando bane, kuma a yanzu muna samun cigaba. A yau muna da Gong, kuma zamu samu Karin wasu kwararrun a nan gaba," Dell ya kara tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China