in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Keke da wasan tseren keke
2017-05-18 12:32:36 cri


Ire-iren kekuna

Yanzu a duniyarmu ana samun ire-iren kekuna fiye da 15. Wasu daga cikinsu an raba su zuwa gidaje daban daban bisa amfaninsu ga dan Adam. Ga misali, da farko muna da keken da ake amfani da shi don biyan bukatarmu ta yau da kullum, wanda ake kiransa "Utility bicycle" a Turance. Sa'an nan akwai keken da ake amfani da shi musamman ma domin gudu a hanyar dake kan duwatsu, wanda yana tare da giyar irin kamar ta mota. Ta wannan na'urar, mutum ba zai sha wahala sosai ba yayin da yake hawan dutse da keke.

Ban da wannan kuma akwai keken da ake amfani da shi musamman ma domin tseren keke, da wanda ake tuka shi zuwa wuraren shakatawa, gami da wani irin keken da ya hada amfanin keke iri-iri a waje guda, wanda ake kiransa " Hybrid Bike" a Turance. Haka kuma, muna da wani irin keken da a kan yi amfani da shi don nuna wasu fasahohi masu ban hadari, sunansa shi ne BMX.

Ban da wannan kuma akwai irin keken da ake tuka shi a cikin ruwa, da keke mai kujeru 2, wanda zai iya daukar mutane 2 a lokacin guda. Sa'an nan akwai keken da za a iya nade shi don ya zama irin na karami, ta yadda za a iya sanya shi cikin mota a tafi da shi.

Tarihin gasannin tseren keke

Gasar tseren keke ta farko a tarihin dan Adam ta gudana ne a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 1868, inda wani dan kasar Birtaniya mai suna James Moore ya lashe gasar, ta wani keken da aka yi shi da ice, wanda kuma yake da wili na karfe. An ce nisan tseren yana da mita 1200. Sa'an nan gasar tseren keke ta farko wadda ta shafi nisan hanyar dake tsakanin birane biyu, ita ce gasar da aka gudanar tsakanin biranen Paris da Rouen na kasar Faransa,inda James Moore ya sake lashe gasar. Ya shafe awa 10 da minti 40 don kammala tseren mai nisan kilomita 123.

Daga bisani an kera fili na musamman domin tseren keke, domin an fara gano cewa za a iya kara sauri idan ana hawan keke cikin wani fili nu musamman maimakon kan hanyar mota. Yanzu matsayin bajinta a fannin hawan keke cikin sauri da aka samu a fannin hawan keke cikin fili na musamman shi ne, wanda Francois Pervis ya cimma a shekarar 2013 a kasar Mexico, inda daidaitaccen saurinsa ya kai kimanin kilomita 77 kan awa guda. Yayin da matsayin bajinta a fannin maras sauri da aka samu shi ne a wajen gasar ta tseren keke ta kilomita 2350, a wani wuri mai duwatsu na kasar Afirka ta Kudu, inda daidaitaccen saurin da aka samu shi ne kilomita 6.8 kan awa daya. Ta haka za mu iya ganin saurin da ake samun wajen tseren keke yana da alaka matuka tare da wurin da ake gudanar da gasar, da nisan tseren.

Wasu shahararrun 'yan wasan tseren keke

A duk gasannin da suka gudana, a kan samu wasu kwararrun 'yan wasa da suka fito suka nuna kwarewarsu a fannin tseren keke. Ga misali Grant Potter, wani dan wasan kasar Amurka wanda ya kwarre a fannin tseren keke kan hanyar mota. Shi ne shugaban shahararriyar kungiyar tseren keke ta Graner-Stradalli. Da David Zabriskie, wanda shi ma wani dan kasar Amurka ne. Ya taba lashe gasar US National Time Trial Championship har karo 7, gami da gasar Grand Tour har karo 3.

Sai dai kar mu manta da shahararren dan wasan kasar Amukra Lance Amstrong, wanda ya taba lashe gasar Tour de Farance har karo 7 a jere, wato daga shekarar 1999 zuwa ta 2005. Sai dai a shekarar 2012, an fara gano cewa ya dade yana amfani da magani mai kara kuzari a lokacin gasanni. Daga bisani, an soke dukkan lambobin da ya lase tun daga shekarar 1998. Ta haka ya zama wani abin misali ga dukkan 'yan wasa, inda labarinsa ke tunasar musu da kar su keta doka da sha magani mai sa kuzari a yayin gasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China