in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana Selby a matsayin gwarzon dan wasan Snooker na shekara
2017-05-11 11:59:11 cri
An bayyana Mark Selby a matsayin gwarzon dan was na snooker na wannan shekara a lokacin bikin bada lambar yabo da aka gudanar a daren Alhamis din data gabata.

Leicester's Selby ya samu damar kafa tarihi ne a kakar wasanni ta 2016/17, bayan da yayi nasarar lashe wasannin har sau biyar da suka hada da wasan: the Paul Hunter Classic, da International Championship, da UK Championship, da China Open da kuma wasan zakaru na duniya.

Dan wasan mai shekaru 33 a duniya wanda yayi nasarara lashe wasannin duniya a karo na uku cikin wannan mako, ya samu kyautar kudi mafi yawa a wannan kakar wasannnin wanda ya tasamma fam 932,000, kuma yayi nasarar zama zakaran wasa na duniya.

Selby ya kuma dauki lambar yabo da yan jaridu yan wasan Snooker na shekara da kuma nay an wasan shekara, wanda ya hada da tafka mahawara game da wasannin a shafukan sada zumunta.

Yan Bingtao dan kasar Sin, mai shekaru 17, yayi nasarar lashe lambar yabo ta Sabon shiga a harkar wasa na wannan shekara bayan namijin kokari da dan wasan ya nuna a kakar wasannin inda ya samu damar matsayi 16 na karshe cikin jerin wasanni 7, a wasani na duniya karo na 56 kuma yayi nasarar fita ta farko a wasannin.

Wasa na ban mamaki wanda Mark King yayi nasarar lashewa ya biyo bayan jawabi mai ratsa jiki da ya gabatar a lokacin da yayi nasara a wasan da aka bude a arewacin Ireland.

Anthony Hamilton ne ya samu wasan da yafi burgewa na shekara bayan da ya samu matsayi na farko wanda yayi nasara German Masters yana da shekaru 45.

Dan wasan da yayi nasara a karo na shida Jimmy White an gabatar dashi a matsayin gwarzo a wasan snooker, tare da mai watsa labarai da dan jarida Clive Everton.

An gudanar da bikin bada lambar yabon ne a otel din Dorchester dake tsakiyar birnin London.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China