in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan da za a iya bi don koyon fasahar wasan ninkaya
2017-06-08 12:08:22 cri

A fannin wasan ninkaya, gasar tsere ta fara farin jini a karnin 19. A matsayin wani dan wasan ninkaya da ya halarci wata gasar, zai yi kokarin ninkaya da sauri, har ya fi sauran 'yan wasan da suka halarci gasar, kuma zai yi kokarin karya bajintar gasar, idan wata gagarumar gasar ce ta kasa da kasa.

Fasahar da 'yan wasan ninkaya suke bi wajen kara saurinsu, ita ce kokarin rage karfin ruwan na janye jikinsu ta hanyar daidaita motsinsu a cikin ruwa. Kuma kafin a shiga cikin wata gasa, za a sanya 'yan wasa su yi watanni suna samun horo, don su zama masu iya jure wahala sosai. Sai dai kwanaki kafin gasar za a rage lokacin horo, saboda baiwa 'yan wasa damar samun murmurewa. Ban da haka kuma, wasu 'yan wasa a kan yi musu aski don kau da dukkan gashin kai da gashin jiki, ta yadda za a iya taimaka musu samun karin sauri a cikin ruwa.

A wajen gasar Olympics ta lokacin zafi, wadda ta kan gudana a duk shekaru hudu-hudu, 'yan wasa maza da mata kowanensu suna da nau'o'in wasannin ninkaya 16, kuma dukkan su ana gudanar da su cikin wani wurin ninkaya, wato 'swimming pool' a Turance, wanda tsayinsa ya kai mita 50. Dukkan gasanni a fannin wasan ninkaya, ana gudanar da su ne karkashin sa idon hukumar wasan ninkaya ta kasa da kasa, FINA.

Manyan gasanni game da ninkaya

Dukkan wadannan fasahohin wasan ninkaya da ka ambata, suna da bambanci sosai a tsakaninsu. Don haka, da wuya a ce wani ya zama mai kwarewa sosai ta fuskar dukkan fasahohin. Amma matukar a samu kwarewa sosai bisa wata fasahar ninkaya kadai, to, zai iya halartar manyan gasannin wasan ninkaya na kasa da kasa ke nan.

Yanzu gasar a fannin wasanin ninkaya mafi girma a duniya ita ce gasar fid da gwani ta wasannin ninkaya ta duniya da hukumar wasan ninkya ta FINA take shiryawa a shekaru 2-2. An fara gudanar da gasar ne tun daga shekarar 1973, inda ake gudanar da gasannin irin daban daban a dukkan bangarorin wasanni masu alaka da ninkaya, ga misali, tseren ninkaya, da tsallake cikin ruwa, da ninkaya a cikin kogi, da wasan kwallon da ake yi a cikin ruwa, da dai makamantansu.

Ban da wannan gagarumar gasa kuma, kamar yadda muka bayyana a baya, cikin gasar wasanninOlympics, gami da gasar ta kasashe masu renon Ingila ta Commonwealth Games, dukkansu na samar da damammaki ga kwararrun 'yan wasan ninkaya na kasashe daban daban, domin su nuna kwarewarsu a fannin wasan ninkaya.

Matakan da za a iya bi don koyon fasahar ninkaya

To, amfanin ninkaya a fannin kiyaye lafiyar jikin dan Adam ke nan. Sai dai kafin a samu wannan amfani, dole ne a fara wasan ninkaya shi da kansa. Don taimakawa wadanda ba su san fasahar ninkaya ba tukuna, na dan takaita wasu matakan da za a iya bi domin koyon fasahar ninkaya. Kuma zan ba da misali da wasan ninkaya na Breaststroke.

Da farko dai, za a fara da koyon fasahar kasancewa kan ruwa, wato ba tare da nutsewa cikin ruwa ba. Don samun wannan fasaha, za a iya tsaya a cikin ruwa maras zurfi, a tsai da numfashi bayan shakar iska. Sa'an nan a tsuguna domin gwada yadda ake tasowa kan ruwa. Bayan da aka fara zama kan ruwa, to, za a iya mika hannaye da kafafuwa, sai dai za a ci gaba da tsai da numfashi.

Bayan da aka samu tasowa kan ruwa, za a iya koyon fasahar numfashi yayin da ake iyo. Abin da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne, kar a yi numfashi karkashin ruwa. Wato duk lokacin da ake numfashi, tilas ne a yi kokarin daga jiki domin kan mutum ya fito daga cikin ruwa, sa'an nan a yi numfashi. Don koyon fasahar wasan ninkaya na Breaststroke, alal misali, za a yi amfani da dukkan hannayen mutum 2 domin a tura ruwa zuwa kasa, ta yadda za a daga kirji da kan mutum zuwa sama, yayin da sauran sassan jikinsa sun ci gaba da kasancewa cikin ruwa.

Bayan an san fasahar zama kan ruwa, da numfashi yayin ninkaya, to, za a koyi fasahar tura jiki gaba bisa mika kafafuwa da karfi, sa'an nan a hade su cikin sauri. A karshe za a hada wadannan matakai da na bayyana tare, a yi su daya bayan daya. Ga misali, za a fara da mika da hade kafafuwa, a sanya jikin mutum ya fara shawagi cikin ruwa, daga baya a tura ruwa da hannaye don daga jiki, sa'an nan a shaki iska, a sake tsunduma cikin ruwa, a fito da iska, a kuma koma matsaki na farko, wato mika da hade kafafuwa. Ta wannan hanya, za a dinga sanya jikin mutum ya ci gaba a cikin ruwa, wato ya fara ninkaya ke nan. Sai da abun nan ba abin da za a iya koya bisa sauraron bayani ba, dole ne a shiga cikin ruwa a gwada da kansa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China