Mai Magana da yawun gwamnatin Sudan Ahmed Bilal Osman, shi ne ya bayyyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya jaddada aniyar gwamnatin kasar cewa a shirye take ta shiga shirin maido da tattaunawar zaman lafiyar a duk lokacin da masu shiga tsakani na Afrika suka tsayar da lokacin.
Sannan ya bukaci yan tawayen na SPLM/ tsagin arewaci dasu warware sabanin dake tsakainsu, wanda ya bayyana shi a matsayin babban shamaki dake iya kawo cikas game da shirin tattaunawar zaman lafiyar a bangarorin kasar biyu.
A ranar Alhamis ne, majalisar Nuba Mountains Liberation Council wato (NMLC), wanda itace majalisar dokokin SPLM/, ta yanke shawarar tunbuke shugabanta Malik Agar, inda ta maye gurbinsa da tsohon mataimakinsa Abdel Aziz al-Hilu.
Wannan mataki ya zo ne, bayan taron ganawar da NMLC ta shirya, wanda al-Hilu ne ya kira taron.