in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin 'yan tawaye sun bukaci a kyale dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfur
2017-06-16 09:45:48 cri
Jagororin kungiyoyin 'yan tawaye biyu dake yankin Darfur na kasar Sudan, sun yi kira ga kwamitin tsaron MDD da kar ya amince da janye dakarun wanzar da zaman lafiya dake aiki a yankin Darfur.

Kafar Sudan Tribune ta rawaito wakilan kungiyoyin na jaddada bukatar barin rundunar (UNAMID) ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta a yankin.

A ranar Laraba ne dai kwamitin na tsaro ya yi zaman tattaunawa game da rahoton babban magatakardar MDD Antonio Guterres game da yankin na Darfur, rahoton da ya amince da rage yawan dakarun sojin rundunar ta UNAMID a karo biyu.

Mr. Guterres ya amince da rage bataliyoyin rundunar 8, cikin jimillar 16 da ake da su a cikin watanni 6 masu zuwa, sa'an nan a janye ragowar bataliyoyin a farkon shekarar badi.

UNAMID dai ta karbi aikin wanzar da zaman lafiya a yankin na Darfur daga hannun tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka AU, a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2007. Wannan runduna kuma ita ce ta biyu mafi girma a duniya, bayan ta janhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Rundunar ta UNAMID dai na kunshe da sojoji sama da 20,000, da 'yan sanda da kuma sauran jami'ai fararen hula, a kuma shekarar 2013 an yiwa tawagar kasafin kudi na dalar Amurka miliyan 1.4. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China