in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka shirya kaiwa masallaci mai alfarma dake birnin Makka
2017-06-25 12:38:17 cri
Gwamnatin kasar Sudan ta yi Allah wadai da harin ta'addaci da aka shirya kaddamarwa kan masallaci mai alfarma dake birnin Makka a kasar saudiyya.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar, ta yi Allah wadai da babbar murya game da yunkurin kitsa harin ta'addanci a ranar Juma'a kan masallacin ka'aba dake birnin Makka a kasar Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Sudan ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin kasar Saudiyya game da dukkan matakan da take dauka wajen tabbatar da tsaro da kare alfarmar masallaci mafi daraja da kare tsaron al'ummar kasar da bakin dake halartar kasar domin gudanar da ibadu daga dukkan ayyukan yan ta'adda da bata gari.

Sanarwar ta bayyana cewa, Sudan ta jinjinawa jami'an tsaron kasar Saudiyyar bisa jajurcewarsu wajen kakkabe duk wani harin ta'addanci, inda ta bayyana laifukan da cewa sun cin karo da koyarwar duk wani addini kuma sun keta hakkin dan adam.

A ranar Juma'a mai Magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Saudi Mansour al-Turki ya bayyana cewa, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar dakile harin ta'addancin da aka shirya kaiwa masallaci mai alfarma dake birnin Makka.

Mansour al-Turki ya ce, jami'an tsaron Saudi sun damke mutane biyar cikin har da wata mata da ake zarginsu da kitsa harin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China