in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe masu tasowa sun nuna yabo ga kudurin Sin na tabbatar da hakkin bil'adam ta hanyar samun ci gaba
2017-06-27 09:30:26 cri
A jiya Litinin 26 ga wata, wakilinmu ya sami labari daga tawagar zaunannen ofishin Sin a MDD dake Geneva, da sauran kungiyoyin duniya na Switzerland cewa, a ranar 22 ga watan nan, majalisar kare hakkin bil'adam ta MDD ta zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar na "tabbatar da kare hakkin bil'adam ta hanyar neman samun ci gaba". Kasashe masu tasowa sun nuna yabo tare da tsaya wa wannan kuduri.

Kasashe masu tasowa suna ganin cewa, wannan kuduri ya bayyana bukatunsu, ya kuma sa kaimi ga hadin kansu, da kara karfinsu na fadin albarkacin baki, da ikon sarrafa sha'anin kare hakkin bil'adam na duniya, da kara kwarin gwiwar kasashe masu tasowa, da kuma ba da jagoranci mai dacewa ga majalisar kare hakkin bil'adam, don haka lamarin ya zama babbar nasara a gare su a wannan fanni.

Zaunannen wakilin Venezuela a MDD dake Geneva, Jorge Valero ya ce, wannan kuduri ya bayyana cewa, bunkasuwa za ta ba da babbar gudummawa ga tabbatar kare hakkin bil'adama, kuma hakan ya dace da jimlolin sanarwar MDD. Kaza lika kasar Venezuela na fatan nuna goyon baya, da mai da martani ga wannan kuduri tare da kasar Sin, kuma za ta yi kokari domin cimma burin samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030, da sa kaimi ga bunkasuwar hakkin bil'adam a dukkanin fannoni.

A nasa bangare, zaunannen wakilin Cuba a Geneva, Raul Pedrozo ya bayyana cewa, Cuba ta nuna godiya ga Sin bisa fitar da wannan kuduri, wanda ya bayyana wani ra'ayin dake samun amincewar duniya cewa, bunkasuwa za ta ba da babbar gudummawa ga tabbatar da hakkin bil'adam. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China