A yayin taron, kwararrun kasar Sin sun bayyana ra'ayin makomar bai daya ta bil Adama daga fannonin kalubalen da ake fuskanta a yanzu, da ra'ayoyin kare hakkin bil Adama, da yadda ake kiyaye hakkin bil Adama bisa tsarin makomar bai daya ta dan Adam, da rawar da Sin ke takawa wajen gudanar da harkokin hakkin bil Adama na duniya, da manufofin da Sin ke bi a fannin addinai da ayyukan da ta zartar wajen samar da makomar bil Adama ta bai daya.
Kana wakilan da suka fito daga kasashen Rasha, da Pakistan da Cuba da dai sauransu, sun gabatar da tambayoyinsu a fannonin rawar da kungiyoyin kula da hakkin bil Adam masu zaman kan su a kasar Sin suke takawa, wajen gudanar da harkokin bil Adama na duniya, sun kuma tattauna matuka tare da kwararrun kasar ta Sin. (Bilkisu)