in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Sin da na waje sun amince da ci gaban da Sin ta samu ta fuskar saukaka fatara
2016-12-05 10:30:04 cri
A jiya Lahadi a nan birnin Beijing, aka bude taron kara wa juna sani na kasa da kasa dangane da cika shekaru 30 da zartas da sanarwar hakkin samun bunkasuwa. Kwararrun ilmin hakkin bil Adam na kasar Sin da na kasashen ketare da suka halarci taron sun amince da ci gaban da kasar ta Sin ta samu ta fuskar saukaka fatara.

Shugaban sashen kula da hakkin samun bunkasuwa na majalisar kula da harkokin bil Adam ta MDD Zamir Akram ya ce, fitar da al'umma sama da miliyan 700 daga kangin talauci kuma cikin wani gajeren lokaci, wata babbar nasara ce ga kasar Sin. Nauyin da ke bisa wuyan kasa da kasa ne a tabbatar da hakkin samun bunkasuwa cikin adalci kuma ba tare da nuna banbamci ba. Sa'an nan, a saukaka fatara a kasa da kasa ta hanyar gudanar da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.

Shugaban hukumar nazarin hakkin dan Adam na kasar Holland wanda kuma shi ne shehun malami kan harkokin dokoki a jami'ar Utrecht, Tom Zwart yana ganin cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ta fannin saukaka fatara babbar nasara ce da aka samu a tarihin hakkin bil dan Adam. Ya kuma yi nuni da cewa, ba kawai aka samu ci gaban hakkin bil Adam a kasar Sin ta fannin tattalin arziki ba, hatta ma ta bangaren yadda ake mayar da al'umma a gaban kome a kasar.

Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin da ma ma'aikatar harkokin waje ta kasar suka shirya wannan taron kara wa juna sani, kuma jami'ai da masana sama da 150 da suka fito daga kasashe da shiyyoyi da kuma kungiyoyin duniya sama da 40 sun halarci taron. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China