in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fidda rahoto game da kare hakkin bil Adama na kasar Amurka
2017-03-09 15:01:44 cri

Ofishin watsa labarai na majalisar zartaswar kasar Sin ya fidda rahoton shekarar bara, game da yanayin da hakkokin bil adama ke ciki a Amurka.

Rahoton mai taken "Bayanai game da hakkokin bil adama a Amurka a shekarar 2016", tamkar martani ne game da makamancin sa, da sashen lura da al'amuran cikin gidan Amurka ya fitar a ranar 3 ga watan nan.

A nata rahoton, kasar Sin ta ce, Amurka ta sake tafka kuskure, game da bayanan da take yadawa, don gane da yadda Sin ke daukar matakai na kare hakkin bil adama.

Rahoton na Sin ya ce, Amurka ta cika takardu da zargi, tare da nuna yatsa ga kasashe da dama a wannan fanni, duk da cewa ba ta maida hankali ba, game da tarin matsalolin da take fuskanta a cikin gida game da kare hakkokin bil adama.

Rahoton ya buga misalai da yadda ake samun yawan harbe harbe na kan mai uwa da wabi a sassan Amurka, da kara tsanantar ayyuka na nuna wariyar launin fata, tare da tsarin siyasa da na 'yan jari hujja. Rahoton ya ce, da irin wadannan tarin abun kunya, bai dace ma Amurka ta samu bakin nuna yatsa ga wasu kan batun kare hakkin bil adama ba.

A daya bangaren kuma rahoton ya bayyana cewa, Amurkar na sahun gaba, wajen yawan firsunoni dake zaune a gidajen yari, inda duk cikin al'ummar kasar 100,000 ake samun mazauna gidan yari 693.

Har ila yau laifuka masu alaka da harbe harbe da bindiga na dada yawaita a kasar. Bisa wasu alkaluma, a baran an aikata laifuka masu nasaba da harbe harben bindiga, wadanda yawan su ya kai 58,125, ciki hadda wadanda suka shafi mutane da dama har karo 385 a kasar ta Amurka.

Rahoton ya ce, dalilin wadannan harbe harbe, mutane 15,039 sun rasa rayukan su, baya ga wasu 30,589 da suka jikkata. Bugu da kari a cikin duk Amurkawa 7, daya na cikin matsanancin talauci, adadin da ya kai kimanin Amurkawan miliyan 45, kamar dai yadda wannan rahoto na Sin, ya hakaito hakan daga jaridar Daily Mail ta Amurka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China