in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin kare hakkin bil-Adama
2015-06-08 10:31:45 cri
Wata takardar sanarwa da ofishin yada labarai na majalissar zartaswar kasar Sin ya fitar, ta nuna irin ci gaba da kasar Sin ta samu a ayyukan kare hakkokin bil-Adama cikin shekarar da ta gabata.

Takardar ta ce a shekarar 2014, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a wannnan fanni, bisa biyayyar ta ga halin musamman na gurguzu, wanda ke maida hankali ga kare doka da oda, da kuma martaba rayuwar al'umma. Kaza lika takardar ta bayyana dacewar tsarin da Sin take bi, wanda shi ne ya haifar da irin nasarar da ake gani a halin yanzu.

Bugu da kari takardar ta ce a shekarar ta bara, kasar Sin ta cimma nasarar dukkanin muradu 12 cikin 29 da ta sanya a gaba, wadanda suka jibanci bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, kudurorin da ke kunshe cikin kaso na 12, na shekarar 2011 zuwa 2015. Kaza lika akwai wasu kudurorin 3 dake daf da kammala, yayin da ake ci gaba da aiwatar da ragowar 11.

A bangaren shari'a kuwa, kasar ta Sin ta gudanar da managartan sauye-sauye, inda shugabannin JKS suka fidda wani sabon shiri na inganta bin doka da oda, yayin taron su na watan Oktobar da ya shude.

Karkashin wannan tsari an karfafa batun kare hakkokin fararen hula, da martaba kimar bil-Adama, da sauran batutuwa masu alaka da hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China