Babban mai kididdiga na Najeriya Yemi Kale, ya bayyana wa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, idan dukkan farashi a kasar bai samu tangarda ba, ciki har da rikicin yankin Niger Delta, daga nan zuwa shekarar 2018 tattalin arzikin kasar zai iya komawa hayyacinsa.
Ya ce, Najeriya ta sha fama da matsanancin halin rikicin tattalin arziki, amma a halin yanzu alamu sun fara nuna cewa kasar ta fara fita daga halin matsin tattalin arzikin, ya ce Najeriya za ta fita daga halin matsin tattalin arziki nan da shekarar 2018.
Kale ya shedawa 'yan jaridu cewa, Najeriya ta fuskanci halin matsin tattalin arziki mafi muni, sai dai sannu a hankali tana farfadowa.
Ya ce tashin farashin kayayyaki a kasar ya ragu zuwa kashi 16.25 cikin 100 a watan Mayu idan aka kwatanta da kashi 17.24 cikin 100 a watan Afrilu.
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce, wannan shi ne faduwar farashi da kasar take samu sau hudu a jere tun daga watan Janairu. (Ahmad Fagam)