Bayan aukuwar zaftarewar kasa a yankin, gwamnatin kasar Sin ta dukufa aikin ceto a wannan yankin, bisa umarnin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar, wanda ya nemi lardin Sichuan ya dukufa wajen aikin ceton mutanen da suka rufta, domin rage adadin wadanda ka iya rasa rayukansu, da yin rigakafin sake aukuwar iftila'in da kuma kiyaye al'ummar yankin yadda ya kamata.
Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin ta aike da tawagar musamman zuwa wurin domin jagorantar aikin ceto da kuma jajantawa al'ummar yankin. (Maryam)