Mista Kiir ya ce, a kasarsa wato Sudan ta Kudu, akwai 'yan gudun hijira da dama da ke bukatar tallafi daga kasashe daban-daban, inda ya ce gwamnatin kasar ba ta da matsala sam, wajen taimakawa hukumomin bada agajin jin-kai gudanar da ayyukansu.
A nasa bangaren, Mista Hailemariam ya nuna cewa, yawan tallafin da kasashe daban-daban suka samar bai isa ba, kuma ya kamata kasashen dake yankin kahon Afirka su inganta hadin-gwiwa ta fuskar tunkarar fari.
A watan Janairun bana, gwamnatin kasar Habasha ta fitar da wani rahoto, inda ta nemi tallafin dala miliyan 950, domin taimakawa 'yan kasar sama da miliyan 5 da matsalar fari ta shafa.
A 'yan shekarun nan, wasu kasashen Afirka na fama da matsanancin fari, ciki har da Habasha, da Sudan ta Kudu, da Kenya, da Somaliya, da Tanzaniya da kuma Uganda.(Murtala Zhang)