in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaftarewar kasa ta binne mutane sama da 140 a kudu maso yammacin kasar Sin
2017-06-24 12:48:35 cri
Majiyoyi daga hukumomin yankin Maoxian na cewa, zaftarewar kasa da ta auku a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin da safiyar yau Asabar agogon kasar, ya rusa gidaje 46, inda ake fargabar ya rufta da mutane 141.

Zaftarewar ya auku ne sanadiyyar faduwar wani dogon tsauni na yankin kabilar Tibetan da Qiang na Aba mai cin gashin kai, akan kauyen Xinmo da misalin karfe 6 na safiya, inda ya tokare bakin wani kogi da nisan kilomita 2.

Har yanzu dai ana ci gaba da aikin ceto. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China