Kusan 'yan Najeriya dubu 240 ne a yanzu haka suke gudun hijira a Kamaru, Chadi da Nijar, kasashe uku makwabta da dukkansu suke kasashe na yankin tafkin Chadi, kamar ita Najeriya, in ji Sani Datti, kakakin hukumar kula da matsalolin gaggawa ta Najeriya (NEMA) a ranar Litinin.
Mista Datti ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, adadin 'yan gudun hijirar Najeriya a cikin wadannan kasashe uku ya cimma jimillar 239.834.
'Yan Najeriyan sun tsere daga yankunansu na jihohin Adamawa, Borno da Yobe dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, dalilin hare haren kungiyar Boko Haram, in ji jami'in.
'Yan Najeriya da suka kaura sun sami tallafin jin kai na kasashen da suka karbe su, daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, al'ummomin wadannan kasashe da kuma 'yan Najeriya dake zaune a cikin wadannan kasashe uku, in ji mista Sani Datti. (Maman Ada)