Mataimakin Gwamnan jihar, Martin Babale ne ya bayyana haka, jiya Laraba a garin Yola babban birnin Jihar, lokacin da yake yi wa manema labarai bayani game da abubuwan da aka cimma a taron majalisar tsaro ta jihar
Ya ce gwamnati za ta dauki matakai da suka hada da karfafawa 'yan gudun hijirar komawa kauyukansu, tare da hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da daga nan zuwa ranar 30 ga watan Junairu, dukkan 'yan gudun hijirar sun bar sansanonin,.
Mataimakin Gwamnan ya ce, ci gaba da zaman 'yan gudun hijira a sansanonin bayan kwace iko da duka garuruwan da rikicin ya shafa, abu ne da zai rage darajar jihar. (Fa'iza Mustapha)