in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan cimma daidaiton kasuwanci da zuba jari tsakanin ta da Amurka
2017-05-25 19:24:43 cri

Wani rahoto da ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar a Alhamis din nan, ya nuna fatan da kasar ke da shi game da gudanar da huldar cinikayya, da zuba jari mai cike da daidaito tsakanin ta da Amurka.

Rahoton ya ce nan gaba, Sin na da nufin hada gwiwa da Amurka, ta yadda kamfanonin Sin za su samu cikakkiyar dama ta shiga a dama da su, a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa, tare da kara budewa juna kofar kasuwanci, da inganta fannonin zuba jari na moriyar juna, tare da bunkasa yarjeniyoyin da ke tsakanin su, ta yadda za a kai ga karfafa hadin gwiwar sassan biyu a bangaren tattalin arziki da zuba jari a matakin shiyyoyi.

Babban burin da ake fatan cimmawa dai bai wuce karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu ba a fannin tattalin arziki da cinikayya.

Har ila yau rahoton ya bayyana aniyar kasar Sin, ta kara yawan kayan da take shigowa da su daga Amurka, musamman wadanda suka shafi makamashi, da albarkatun gona, da fannonin zurfafa fasahohi da na bada hidima, ta yadda hakan zai samar da irin daidaiton da ake fata tsakanin kasashen biyu a bangaren inganta cinikayya da zuba jari.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China