Shugaba Xi ya bayyana hakan ne ga mambobin kwamitin jam'iyyar ta kwaminis, da ma sauran jagorori a fannoni masu nasaba da samar da ci gaba. Ya kuma ce taron da ke tafe na da matukar muhimmanci ga ci gaban jam'iyyar, da ma tsarin siyasar kasar baki daya.
Shugaban Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin zartaswar JKS, ya yi tsokacin ne yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin. (Saminu Hassan)