Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino, a yau Laraba a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar tasu, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan raya harkar wasan kwallon kafa a kasar. A shekarun baya, kasar Sin ta yi kokarin janyo hankalin jama'a domin su fara rungumar wasan kwallon kafa, haka kuma ta dauki matakan daidaita tsarin da ake bi wajen gudanar da harkokin kuloflikan wasan kwallon kafa na kasar.
A nasa bangaren, mista Infantino ya ce yadda ake samun ci gaba a fannin wasan kwallon kafa a nan kasar Sin yana da ma'ana sosai. A madadin hukumarsa, ya nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin bisa kokarin da ta yi wajen raya harkar wasan kwallon kafa a kasar.(Bello Wang)