Wang Yi ya bayyana cewa, wannan ne ziyara ta farko bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci dandalin tattaunawar hadin gwiwar "ziri daya da hanya daya", kana ita ce muhimmiyar ziyarar diplomasiyya ta kasar Sin a yankin Asiya da Turai. A cikin awoyi fiye da 60 da suka wuce, shugaba Xi ya halarci bukukuwa fiye da 20, inda aka tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Kazakstan, da hangen makomar bunkasuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai tare da halartar bikin baje koli na duniya na Astana. Ziyararsa tana shaida tunanin hanyar siliki wato hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa, da koyi da juna, da samun moriyar juna, da sa kaimi ga inganta "ziri daya da hanya daya" da hada kan juna don shimfida zaman lafiya da samun wadata a yankin. (Zainab)