in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi a taro karo na 17 na majalisar shugabannin kasashe mambobin SCO
2017-06-10 11:31:27 cri
Taro karo na 17, na majalisar shugabanin kasashe mambobin kungiyar hadin kan Shanghai wato SCO a takaice, da ya gudana jiya Juma'a a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan, ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwarorinsa na Kazakhstan Nursutan Nazarbaev, da Kyrgyzstan Almazbek Atambayev, da na Rasha Vlładimir Putin, da Tajikistan Emomali Rakhmonov, da kuma na Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev.

A yayin taron, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "hada kai da bude kofa ga juna don kafa gida na bai daya mai karko da wadata".

A cikin jawabin na sa, shugaba Xi ya bada da shawarwari a fannoni biyar, da suka hada da inganta hadin kai da tinkarar kalubale tare da zurfafa hakikanin hadin kai da kara cudanyar al'adu, da kuma tsayawa kan bude kofa da yin hakuri da juna.

A nasu bangaren, shugabannin da suka halarci taron sun yi maraba da shawarar "Ziri daya da hanya daya", inda suka yaba da sakamakon da aka samu a dandalin tattaunawar hadin kai na kasa da kasa game da shawarar, wanda aka shirya a watan Mayun da ya gabata a nan Beijing, tare kuma da goyon bayan tabbatar da ra'ayin bai daya da aka cimma. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China