in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da ministocin kasashe uku
2017-06-19 10:12:59 cri
A jiya Lahadi ne, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya gana da ministan dangantaka da hadin gwiwa da kasashen duniya na kasar Afirka ta Kudu, Maite Nkoana-Mashabane, da ministan harkokin waje da na gida na Indiya, Vijay Kumar Singh, da kuma ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov a birnin Beijing, wadanda ke halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS.

A yayin ganawarsa da minista Maite Nkoana-Mashabane, Wang ya ce, Sin na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu, da kokarin raya tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da kungiyar kasashen BRICS, domin kyautata ma'anar hadin gwiwa tsakaninsu bisa manyan tsare tsare, da tabbatar da moriyar kasashen biyu da na sauran kasashe masu tasowa baki daya.

A yayin ganawarsa da minista Vijay Kumar Singh na kasar Indiya, mista Wang ya furta cewa, a matsayinsu na manyan kasashe biyu dake da babban tasiri ga duniya, Sin na fatan taka muhimmiyar rawa tare da kasar Indiya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya shiyya da ma duniya baki daya.

Bayan haka, a yayin ganawarsu, mista Wang ya bayyana wa minista Sergei Lavrov na Rasha cewa, Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Rasha, da gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS karo na farko lami lafiya tare da juna, da kuma shirya taron shugabannin kasashen BRICS da za a yi a birnin Xiamen dake nan kasar Sin yadda ya kamata.

Ministocin uku sun bayyana fatansu na yin hadin gwiwa da Sin, ta yadda za a samu nasarar taron shugabannin kasashen BRICS na birnin Xiamen.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China