Na farko shi ne, ya fara ziyararsa bayan taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "Ziri daya hanya daya", sa'an nan, dukkanin kasashen hudu da ya ziyarta sun bayyana fatansu na shiga ginawar shawarar. Don haka yana ganin cewa, wannan ba kawai fatan wadannan kasashen Afirka guda hudu ba ne, har ya zama fatan dukkanin kasashen nahiyar Afirka. Haka kuma, ya ce, kofa a bude ta ke ga duk wanda ya amince da wannan shawara, da wande yake son zama abokan hadin gwiwa.
Na biyu shi ne, ya sha kai ziyarar aiki kasashen Afirka, inda ya fahimci fatan kasashen Afirka na gaggauta raya harkokin masana'antunsu, ta yadda za su kara karfinsu na samun ci gaba da kansu, ta yadda za su samu 'yancin tattalin arziki. Kasar Sin tana fatan taimakawa kasashen Afirka a wannan fannin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Na uku kuma, lalle an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma dadaddiyar huldar abokantaka dake tsakaninsu.
A karshe, ya ce, nahiyar Afirka tana da makoma mai kyau, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga 'yan uwanta na kasashen Afirka, domin su cimma burinsu cikin sauri na samun kyakkyawar makoma a nan gaba. (Maryam)