in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kasuwancin Amurka ya alkawarta kulawa da jarin da kamfanonin kasar Sin dake Amurka
2017-06-21 19:48:15 cri
A jiya Talata, ministan kasuwancin kasar Amurka Wilbur Ross, ya alkawarta cewa, za a kula da jarin da kamfanonin kasar Sin ke zubawa a kasar Amurka cikin adalci.

Mr. Ross ya fadi hakan ne a yayin da yake jawabi a wani bikin liyafar da babbar kungiyar 'yan kasuwa ta Sinawa dake kasar Amurka ta shirya wa masu zuba jari a kasar. Kazalika, Mr. Ross ya gode wa tawagar wakilan mazu zuba jari na kasar Sin wadanda suka halarci taron koli na zuba jari mai jigon "Zabin Amurka" na shekarar 2017.

A tsakanin ranekun 18 da 20 ga watan nan na Yuni ne ake taron koli na zuba jari mai jigon "Zabin Amurka" na shekarar 2017, a jihar Mariland dake kusa da birnin Washington DC, fadar mulkin kasar Amurka.

Bisa umarnin matakin farfado da sana'o'in kere-keren kasar Amurka da shugaba Donald Trump ya gabatar, yanzu haka daga gwamnatin tarayyar zuwa kananan hukumomi na gwamnatoci a matakai daban daban dake kasar Amurka, na kokarin jawo jarin waje da kuma 'yan kasuwa baki, tare da kokarin kafa wani kyakkyawan yanayi na shigar da jarin waje cikin kasar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China