in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila za a dakatar da shirin ziyarar Trump a kasar Birtaniya domin jama'ar kasar Birtaniya suka ki amincewa da shi
2017-06-12 20:37:28 cri
Jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta ruwaito a yau cewa,watakila za a dakatar da ziyarar da shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kai kasar Birtaniya a bana saboda jama'ar kasar Birtaniya ba su amincewa da ita ba, firaministar kasar Birtaniya Theresa May za ta gabatar da wannan labari a 'yan kwanaki masu zuwa.

Amma kakakin fadar firaministar kasar Birtaniya ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, yanzu ba a canja shirin gayyatar da aka yiwa Trump zuwa kasar Birtaniya ba.

Jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta bayar da labari a jiya cewa, Trump ya bayyana yayin da yake waya da Theresa May cewa, ba zai kai ziyara kasar Birtaniya ba sai jama'ar kasar Birtaniya sun goyi bayan ziyarar. Amma rahoton bai nuna daga ina wannan labari ya fito ba (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China