Sai dai Shugaban Amurkan ya ce, kasar ba za ta rufe ofishin jakadancinta a Cuba, wanda ta sake bude shi a shekarar 2015 ba.
Donald Trump ya yi wannan jawabi ne a birnin Miami na jihar Florida, inda ya ce yarjejeniyar da gwamnatin Obama ta kulla da kasar Cuba, ba ta yi wa Amurka adalci ba, don haka za a soke ta nan take.
Baya ga haka, za a hana kamfanonin Amurka mu'amala da wasu kamfanonin kasar Cuba wadanda ke karkashin kulawar sojojin kasar. Sannan za a tsaurara sharadi don takaitawa jama'ar Amurka zuwa yawon bude ido a Cuba.
Haka zalika, Trump ya jaddada cewa, Amurka za ta ci gaba da sanya takunkumi a fannonin tattalin arziki da hada-hadar kudi da cinikayya a kan kasar Cuba.
Bayan wannan jawabi ne shugaba Trump ya rattaba hannu kan umarninsa dangane da sabuwar manufar Amurka a kan kasar Cuba.(Bello Wang)