Da yake bayyana hakan yayin wani taron manema labarai yau Laraba a nan birnin Beijing, Mr. Geng ya ce za a gudanar da taron ne tsakanin ranekun 26 zuwa 28 ga watan Yunin nan.
Mahalarta taron za su hada da jagorori daga kasashen Finland da Sweden, da wakilai da dama da za su yi musayar yawu game da harkokin cinikayya da na kasuwanci. Kaza lika masana da masu fashin baki tare da 'yan jaridu su ma za su halarci taron.
Taron na bana dai na da taken "samar da ci gaba daga dukkanin fannoni, a yayin sauyi na hudu na ci gaban masana'antu". (Saminu Hassan)