in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a sa ido kan sauyin masana'antu karo na hudu a yayin taron Davos na lokacin zafi na bana
2016-06-17 09:51:43 cri
Jiya, 16 ga wata, hukumar shirya taron tattaunawar tattalin arzikin duniya ta Davos ta shelanta a hedkwatarta dake Geneva, cewar za a yi taron shekara-shekara karo na 10 na lokacin zafi na Davos a birnin Tianjin na kasar Sin a tsakanin ranukan 26 da 28 ga watan nan. Babban jigon wannan taron shekara-shekara shi ne "sauyin masana'antu karo na hudu: karfin neman sauye-sauye".

Hukumar dake shirya wannan taro ta bayyana cewa, a yayin taruruka fiye da 200 da za a yi a cikin kwanaki 3, shugabanni fiye da 1700 na hukumomin gwamnati da hukumomi masu zaman kansu wadanda za su fito daga kasashe 90 da sauran yankunan duniya za su tattauna kan yadda za a iya fahimtar sauyin masana'antu karo na hudu, kuma za su yi kokarin neman hanyoyin da za su dace da irin wannan sauyi. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China