Maganar da firaministan kasar Sin ya fada ta janyo hankalin baki fiye da 1000 na kasashen waje dake halartar dandalin Davos na wannan karo. Wasu daga cikinsu kuma sun bayyana imanin da suke da shi kan tattalin arzikin kasar Sin.
Jan Mladek, ministan masana'antu da cinikayya na kasar Czech, ya ce dalilin da ya sa yake da imani kan tattalin arzikin kasar Sin shi ne domin, na farko, kasar Sin na kokarin zaman dacewa da yanayin da ake ciki na raya kimiyya da fasaha, sa'an nan na biyu shi ne, har yanzu kasar na daidaita tsarin al'ummarta, kuma mutanen dake kauyuka da yawa za su fara zama ma'aikata.
A nasa bangare, Ditshego Tladi, shugaban wani kamfanin kasar Afirka ta Kudu, ya ce, a ganinsa tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da karuwa, kana matakan da gwamnatin kasar ta dauka sun janyo hankalin wasu kamfanoni na kasashen waje da yawa domin su zuba jari a kasar.(Bello Wang)